Zaman lafiya ya dawo a babban birnin Chadi da safiyar yau Alhamis, bayan da wasu mahara dauke da muggan makamai suka afkawa fadar shugaban kasar, abinda ya sabbaba artabun daya hallaka mutane 19, galibinsu maharan, a cewar gwamnatin kasar.
An janye karin jami’an tsaron da aka jibge da shingayen binciken ababen hawan da aka kafa a yankin dake kewaye da fadar shugaban kasar, inda zirga-zirgar ababen hawa ta koma kamar yadda aka saba, kamar yadda wakilan kamfanin dillancin labarai na AFP suka gano.
Zazzafar musayar wuta ta barke a kusa da ginin fadar shugaban kasar dake tsakiyar N’djamena, babban birnin kasar ta tsakiyar Afrika dake karkashin mulkin soji, ‘yan mintunan kalilan kan karfe 8 na dare agogon Chadi.
Kakakin gwamnatin kasar Abderahaman Koulamallah yace mambobin rundunar sojin Kundunbala 24 dauke da “bindigogi da adduna da wukake” sun farwa dogarawan tsaron fadar shugaban kasar kafin a yanke musu hanzari cikin sauri.
A wani bidiyon da aka nada bayan faruwar lamarin kakakin gwamnati, ministan harakokin wajen kasar Abderamane Koullamala ne ya bayyana a tsakiyar farfajiyar fadar shugaban kasa da bindiga daure a kugunsa ya tabbatar da cewa askarawan gwamnati sun dakile wannan farmaki.
Daga bisani ministan ya bayyana a gidan talbijan mallakar gwamnatin Chadi domin yi wa ‘yan kasar karin bayani.
"Sun danna kai a cikin fada, askarawa suka bude masu wuta kuma nan da nan aka gama da su. 18 daga cikinsu sun sheka lahira sai wasu 6 da a halin yanzu ke hannun mashara’anta, abin ya na da daurin kai" inji kakakin gwamnati Koullamala wanda ya kawar da zargin harin ta’addanci ne.
"A gaskiya ni ban ga wani tsararren abu ba a wannan harka, na ga layoyi da kiri daure a jikinsu watakila an ce masu bindigogi ba za su harbe su ba amma kuma ba haka abin yake ba.
"Ba zan yi garajen ba da wani ra’ayi a kan wannan al’amari ba domin hurumin mashara’anta ne", inji shi.
Ya kara da cewa Shugaba Mahamat Deby ya umurce mu, mu yi wa ‘yan kasa bayani mu kuma tabbatar masu cewa wannan hari ba shi da wani tasiri, babu wata barazanar da kasa ke fuskanta.
Domin jin halin da ake ciki a washegarin faruwar wannan al’amari Muryar Amurka ta tuntubi AbdoulRazak Garba Baba wani dan jarida mazaunin N’Djamena.
Ganin yadda aka kai wannan farmaki a wani lokacin da dangantaka ta yi tsami a tsakanin Chadi da Faransa bayan da gwamnatin Marechal Mahamat Deby ta umurci Faransar ta kwashe sojojinta daga kasar wasu na alakanta abubuwan biyu.
Saurari rahoton Souley Moumouni Barma:
Your browser doesn’t support HTML5