Matakin na zuwa ne a wani lokacin da shugaban Senegal Bassirou Diomaye Faye ya bada sanarwar rufe sansanonin sojan kasashen waje a hukunce.
Sai dai wasu ‘yan Nijar na kallon abin tamkar wani tsari dake boye wata manufa.
Da yake jawabin barka da sabuwar shekara wa al’ummar kasar ta kafafen labarai a jiya Talata Shugaban kasar Cote d’Ivoire Alassan Ouattara ya sanar da shirin ficewar sojojin Faransa, matakin da ya ce an dauke shi ne a karkashin wani tsarin tuntuba da fahimtar juna a tsakanin gwamnatocin kasashen 2.
A ra’ayin wani mai sharhi a kan al’amuran yau da kullum AbdoulaRazak Ibrahima wannan ba zai rasa nasaba ba da kammalar ayyukan horon da ya kamata dakarun na Faransa su baiwa takwarorinsu na Cote d’Ivoire dai-dai da ajandar ainahi.
Sojojin Faransa kimanin 600 ne ke girke a Cote d’ivoire inda suka shafe gomman shekaru a sansanin Port Boue, kuma a cewar shugaba Ouattara za su fice daga kasar cikin tsari da daraja juna a watan nan na Janairun 2025.
Yayinda tuni aka yanke shawarar damka komai na wannan sansani a hannun sojan Cote d’ivoire.
Sai dai Oumarou Ibrahim Djamilou na cewa akwai wata munufar boye bayan wannan al’amari.
Faransa wace aka kori askarawanta daga Mali, Burkina Faso da Nijar kafin daga bisani Chadi, ta bi sahu na fuskantar koma bayan huldar diflomasiya da kasashen da ta yi wa mulkin mallaka domin kwatsam shi ma shugaba Bassirou Diomaye Faye na Senegal a jawabin barka da shekarar 2025 ya sanar da dauka matakin rufe dukkan sansanonin sojan kasashen waje a kasar, wani matakin da ko shakka babu ke shafar Faransa.
Yanzu dai masu bin diddigin al’amuran tsaro da siyasar kasa da kasa sun zuba ido domin ganin yadda za ta kaya a bisa al’akari da wasu bayanan da ke cewa Faransa ba ta fice kwatakwata ba, asali ma ta fara shirin bullo da sabon salon ajiye dakarunta a wasu kasashe sama da 10 na nahiyar Afirka cikin wani yanayi da ba kowa ke iya fahimtar abin da ke faruwa ba.
Saurari cikakken rahoto daga Souley Moumouni Barma:
Dandalin Mu Tattauna