Manazarta sun ce dalilin da ya sa Ministan Harkokin Wajen China, Wang Yi, ya zabi kai ziyara Jamhuriyar Congo, da Najeriya, da Chadi da Namibiya, a Afirka a wannan makon shi ne batun ma'adanai da man fetur, da sake mayar da hankali kan gabar tekun Atlantika, da kuma tasirin da kasashen yammacin duniya su ke yi a yankin Sahel.
Cobus van Staden, wani editan shirin China Global South Project, ya shaida wa Muryar Amurka a cikin sakon murya ta manhajar WhatsApp cewa, babban abin da ke tattare da hakan shi ne nuna cewa, China aminiya ce ga kowa da ba ta nuna wariya; ba ta da nuna banbanci kamar yadda manyan kasashen yammacin duniya su ke yi.
Kamfanin dillancin labaran China Xinhua ya bayar da rahoton cewa, yayin ziyararsa ta farko a Namibiya a ranar Litinin, Wang ya ce al'adar shekaru 35 na kai ziyara wanda a wannan shekara ya fara da Afirka, ta nuna wa duniya cewa, "China ta kasance amintacciyar aminiyar Afirka" kuma "mafi karfin goyon bayanta.
Dandalin Mu Tattauna