Cutar HMPV: Gwamnatin Najeriya Na Matukar Sanya Idanu - NCDC

Dakin binciken kwakwa na maganin cutar kanjamau

Cibiyar yaki da cututtuka masu yaduwa ta Najeriya (NCDC) ta ce kasar nakan matsakaicin hatsarin yaduwar sabuwar kwayar cutar HMPV mai kama da mura.

A cikin shawarwarin kiyaye lafiyar al’ummar da ta fitar, gwamnatin tarayyar Najeriya ta bayyana cewa tana matukar sa idanu a kan barkewar annobar da kwayoyin cutar “virus” ke yadawa kuma tana daukar matakan kariya da nufin karfafa shirin kasar na tunkura tare da yaki da ita.

NCDC ta kara da cewa “ita da hadin gwiwar hukumar kula da kiwon lafiya a kan iyakokin kasar, na daukar kwararan matakan tunkurar cutar a kan iyakokin kasar na kasa da kasa a matsayin matakin tantance kwayoyin cutar a jikin mutane.

NCDC ta ci gaba da cewa tana gudanar da aikin tantance hatsarin yaduwar cutar ne da hadin gwiwar ma’aikatar lafiya ta tarayyar kasar da hukumomin da ke ba da gudunmowa irinsu hukumar lafiya ta duniya (WHO) da cibiyar yaki da rigakafin cututtuka ta Amurka (USCDC) da takwararta ta Burtaniya (UKHSA)

Ta ce NCDC na kokarin baiwa ‘yan Najeriya “sahihan bayanai a kan lokaci tare da yi musu jagora domin kasancewa a ankare kuma a shirye.”