Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hukumar NCDC Ta Najeriya Ta Ayyana Dokar Ta-Baci Saboda Barkewar Cutar Kwalara


Cholera patients are treated at a local council clinic in Harare
Cholera patients are treated at a local council clinic in Harare

Hukumomin Najeriya sun ayyana dokar ta-baci a kasar tare da kaddamar da matakan dakile yaduwar cutar amai da gudawa da ake kira kwalara, wadda ta hallaka mutane sama da 50.

Cibiyar kare cututtuka ta kasa a Nigeria ko NCDC ta fada a ranar Talata cewa, matakin da ta dauka na maido da cibiyar kula da ayyukan gaggawa na cutar kwalara ta kasa ya biyo bayan nazari kan cutar da hukumomi su ka gudanar a makon jiya, kamar yadda wakilin Muryar Amurka Timothy Obiezu ya bayyana.

NCDC tace, nazarin ya nuna kasar na matakin hadari babba game da cutar, da ya kai yawan mutanen da ke mutuwa daga cutar ta kwalara har kashi 3 da rabi daga cikin 100.

Ya zuwa yanzu dai mutane 53 ne suka rasa ran su da ga cikin wadanda su ka kamu da cutar a kasar su sama da 1,500. Birni mafi girma a Najeriya da hadahadar tattalin arziki, wato Lagos, ke kan gaba a kamuwa da cutar.

“Bayan la’akari da dukkan bayanan da ke kasa, har yanzu akwai alamun samun Karin kamuwa da cutar a ko’ina a fadin kasar. Akwai matakan hadarin kamuwa da cutar har hudu,- matakin kasa kwarai, tsaka tsaki, sai matakin sama da na can sama. An samu karin jihohin da aka kamu da cutar, fiye da yadda muka gani a bara,” a cewar Jide Idris, darakta janar na hukumar NCDC.

Asibitin Bwaila a Lilongwe, Malawi, Jan. 11, 2023.
Asibitin Bwaila a Lilongwe, Malawi, Jan. 11, 2023.

Hukumomin lafiya na kasa sun ce, za su yi aiki tare da hukumomin jihohin da abun ya shafa domin tabbatar da ganin ana gaggauta gano wadanda suka kamu, tantance su da kula da su.

Barkewar cutar ta baya bayan nan na zuwa ne a daidai lokacin da tarayyar Turai ta yi alkawarin taimaka wa da kudin samar da rigakafi a Afrika. Nahiyar ta dogara ne da magungunan rigakafi da ake shugowa da su, da sama da kashi 90 daga cikin 100.

A makon jiya, hukumar ta NCDC tace, Najeriya bata da rigakafin cutar Cholera, amma tana jiran isowar shi.

Chukwunonso Umeh, mai sharhi akan al’amurran kiwon lafiyar jama’a. Ya ce barazanar ba ta wasa bace.

Na yi farin ciki da gwamnati ta ayyana dokar ta baci akan lamarin. Cutar ta yadu matuka, don haka akwai yuwuwar cutar ta rikide ta kara tsanani, ta la’akari da alamunta masu tsanani, da yadda take yaduwa kamar wutar daji,” a cewar Chukwunonso.

Annobar cutar Kwalara a Zambia
Annobar cutar Kwalara a Zambia

Umeh yace, matsalolin rayuwa da na tattalin arziki na shafar yadda cututtuka ke shafar ‘yan Najeriya. Ya kara da cewa, “Cholera cuta ce da ke da alaka da batun tsabta. Ta yanayin ji a jika da ake fama yanzu haka a kasar, mutane kowa yana ta-kai-ta-kai, akwai hadurra da dama da mutane basa iya yin katanga da su. Ba ka iya cewa ga irin ruwan da mutane ke amfani da shi suna dafa wasu daga cikin abincin da suke ci. Daya daga cikin abu mafi muhimmanci a yanzu na rage matsalar shi ne, inganta sha’anin wayar da kan jama’a game da abin da ya kamata su yi, tattara al’umma da fadakar da ita.

Cholera cuta ce da ake samu a Najeriya daga lokaci zuwa, lokaci, dan haka hukumomi suka yi gargadin cewa, matsalar na iya kazanta a yanayi na damina.

Cutar na yaduwa ta gurbataccen abinci da ruwa, da kan haifar da gudawa mai tsanani, har ta kai ga rasa rai idan ba a samu magani ba.

A shekarar 2018, Najeriya ta sanar da samun mutane 830 da suka mutu daga cikin adadin mutane sama da 42,000 da suka kamu da cutar cholera, wannan shi ne adadi mafi yawa da aka gani a ‘yan shekarun nan.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG