CISA: Kutsen Sashen Baitulmalin Amurka Bai Shafi Sauran Hukumomin Gwamnati Ba

CISA

Hukumar Amurka mai sa ido kan al’amuran yanar gizo CISA ta fada a ranar Litinin cewa, babu alamun matsalar kutsen da aka bada labarin cewa sashen baitulmalin Amurka ya fuskanta ya shafi sauran hukumomin gwamnati.

A karshen watan jiya, hukumar baitulmalin Amurka ta ba da rahoto cewa ‘yan China masu kutse sun samu damar shiga wasu na’u’rorin kwamfutan Amurka da ba a tantance adadinsu ba, bayan wani kutse a kamfanin BEYOND TRUST, wanda ya ke kula da tsaron yanar gizo.

Kamfanin na BEYOND TRUST ya fada a makon jiya cewa abokan huldarsa kalilan ne lamarin ya shafa ba tare da yayi Karin bayani ba.

‘Yan Republican a majalisar dokoki sun bukaci a gabatar da bayanai a game da matsalar, na baya bayan nan a jerin kutsen da ake zargin Beijin da aikatawa.