Faduwar Karamin Jirgi Ya Hallaka Mutane 2 A California

Wani Karamin Jirgin Saman Daya Fadi Ya Hallaka Mutane 2 A California

Wani karamin jirgin sama ya rikito kan wani ginin kasuwanci a California a jiya Alhamis, inda ya hallaka akalla mutane 2 tare da jikkata wasu 18, a cewar ‘yan sanda.

Al’amarin ya faru ne da maraice a kusa da tashar jiragen saman birnin Fullerton, mai nisan kilomita 40 daga kudu maso gabashin Los Angeles. ba’a tantance musabbabin faduwar jirgin ba.

“An tabbatar da mutuwar mutane 2,” kamar yadda ‘yan sandan Fullerton suka wallafa a shafinsu na X.

Har ila yau, an kwantar da mutane 10 a asibiti sannan an yiwa wasu 8 magani a wurin da al’amarin ya faru.

Masu bincike basu tantance ko wadanda suka mutun fasinjojin ne ko kuma ma’aikata ne a ginin da jirgin saman ya fada, kamar yadda wani jami’in dan sanda ya shaidawa wata kafar yadan labaran KTLA da ke yankin.