Gwamnatin Austireliya ta fitar da gargadi mai tsauri akan yin balaguro, inda ta bukaci ‘yan kasar dasu sake nazari gabanin yin tafiya zuwa Najeriya.
A sanarwar da ta fitar a yau Talata, ma’aikatar harkokin waje da kasuwancin kasar austireliya (DFAT) ta kafa hujja da halin rashin tabbas a yanayin tsaro da ayyukan ta’addanci da garkuwa da mutane, da kuma yiyuwar barkewar tarzoma a matsayin dalilan ba da shawarar.
An ruwaito shawarar yin balaguron na cewa “ku sake nazarin bukatar yin balaguro zuwa Najeriya saboda rashin tabbas a yanayin tsaro da barazanar ta’addanci da garkuwa da mutane da tashe-tashen hankalin dake da nasaba da miyagun laifuffuka da kuma yiyuwar barkewar tarzoma.
“Akwai hatsarin gamuwa da hare-haren ta’addanci daga kungiyoyin mayaka daban-daban a fadin Najeriya. Hare-haren na iya zama na kan mai uwa da wabi kuma a kan baki ‘yan kasashen waje.
“Ku sake nazari game da bukatarku da zuwa ko’ina a cikin Najeriya, ciki har da babban birnin kasar, Abuja.
Gargadin na zuwa ne sakamakon alkaluman baya-bayan nan da hukumar kididdigar Najeriya (NBS) ta fitar, wacce ta bada rahoton yin garkuwa da mutane sau 2, 235, 954 tsakanin watan Mayun 2023 zuwa Afrilun 2024.
Ku Duba Wannan Ma ‘Yan Nijeriya Sun Biya Dala Biliyan 1.42 Kudin Fansar A Shekara – Cibiyar NBSAn kiyasta jumlar kudin fansar da aka biya a wannan dan tsakani ya kai Naira tiriliyan 2.2, inda a bisa kiyasi kowane mutum ya biya Naira miliyan 2.7.