Uwargidan gwamnan Jahar Filato, Helen Mutfwang ta ba da tallafin ga dattawan a wani shiri da uwar gidan shugaban Najeriya, Oluremi Tinubu ta aiwatar a karkashin shirin Renewed Hope Initiative.
Oluremi Tinubu ta ce shirin zai ci gaba da tallafawa tsofoffi a kowace shekara a jihohi talatin da shida na Najeriya da birnin tarayya Abuja, tare da kuma tsofoffin sojoji da kungiyar matan 'yan sanda.
Matar gwamnan Jihar Filato, Helen Mutfwang ta ce, shugabannin shirin Renewed Hope Initiative sun amince da karin tallafin daga naira dubu dari zuwa naira dubu dari biyu, don tallafawa tsofoffin.
Helen ta ce, naira biliyan daya ne za'a rarrabawa tsofoffin da aka zaba a fadin Najeriya, wanda kowanne dattijo zai sami naira dubu dari biyu.
Uwar gidan gwamnan ta ce banda wadannan kudaden, za'a kuma duba lafiyar tsofoffin kyauta.
Hasiya Abdullahi da Joseph Moses da suka ci gajiyar shirin, sun bayyana farin cikinsu da samun tallafin. Sarah Joseph da Adama Musa suma sun ce, tallafin kudin zai taimaka wa rayuwarsu.
Uwargidan shugaban Najeriya Oluremi Tinubu ta shawarci tsofoffin da su rika cin abinci mai kyau, da shan isasshen ruwa, da motsa jikinsu, sannan su kuma sami isasshen hutu don kara samun kwarin jiki.
Saurari rahoton cikin sauti:
Dandalin Mu Tattauna