Manazarta na ganin hakan zai bunƙasa tattalin arzikin kasar da kuma saukaka farashin kayayyaki a Najeriya.
Yarjejeniyar kudin ta kunshi samar da kudin Najeriya na Naira ga ‘yankasuwar kasar Sin da kuma kudin Yuan ga 'yan kasuwar Najeriya, domin rage dogaro da dalar Amurka ga kasashen biyu.
Sabuwar yarjejeniyar za ta fadada amfani da Naira da Yuan wajen hada-hadar kasuwanci tsakanin kasashen biyu, tare da karfafa hadin gwiwar hada-hadar kudi.
Kasar Sin na daga cikin manyan kasashen da ke alakar cinikayya da Najeriya, kasuwancin da ke tsakanin kasashen 2 sun haɗa da na cinikayyar albarkatun mai, iskar gas, da sauran ma’adinai.
Kazalika, Najeriya na shigowa da kayayyaki da dama daga kasar Sin da suka hada da cinikayyar manyan motoci da motocin alfarma, na’urorin lantarki, da kuma sauran kayayyaki.
Dr. Bature Abdulaziz, shugaban 'yan kasuwa a Najeriya, ya ce “yarjejeniyar musayar kudaden tsakanin kasashen biyu za ta taimaka wajen bunƙasa hada-hadar kasuwanci da kuma rage dogaro da dalar Amurka”.
Abdulaziz ya kara da cewa “hakan ba zai saukaka farashin kayayyaki a Najeriya nan take ba, domin abu ne da ke daukar lokaci kafin a gani a kasa, don haka 'yan kasar kada su zargi 'yan kasuwa wajen kara farashin kayayyaki”.
A hirarsa da Muryar Amurka, Dr. Isa Abdullahi Kashere, manazarcin tattalin arziki da ke jami’ar tarayya ta Kashere a Jihar Gombe, ya ce “yarjejeniyar da Najeriya da kasar Sin suka cimma wajen musayar kudade tsakanin su, za ta bunkasa tattalin arzikin Najeriya, da kuma saukaka farashin kayayyaki”.
A shekarar 2023 Najeriya ta shigo da kayayyakin da suka kai na dalar Amurka biliyan 11.2 daga kasar Sin, kazalika kasar ta fitar da kayayyaki da darajar su ta haura dala biliyan2.4 zuwa kasashen Asia.
Saurari cikakken rahoto daga Rukaiya Basha:
Dandalin Mu Tattauna