Trump Ya Gana Da Shugaban TikTok

Rana guda bayan ziyarar, Tiktok ya bukaci kotun kolin Amurka ta yiwa dokar, da za ta tilastawa mamallakansa ‘yan asalin China sayar da manhajar yanar gizon ta aikewa da sakonnin bidiyo ko kuma rufeta nan da wata guda, dakatarwar wucin gadi.

Shugaban Tiktok ya kaiwa zababben shugaban Amurka Donald Trump ziyara, a cewar rahoton kafar yada labarai ta NBC.

A wani taron manema labarai a jiya Litinin, Trump yace yana kaunar manhajar ta Tiktok kuma gwamnatinsa za ta yi nazarin a kanta da kuma na yiyuwar dakatarwar.

Rana guda bayan ziyarar, Tiktok ya bukaci kotun kolin Amurka ta yiwa dokar, da za ta tilastawa mamallakansa ‘yan asalin China sayar da manhajar yanar gizon ta aikewa da sakonnin bidiyo ko kuma rufeta nan da wata guda, dakatarwar wucin gadi.

Dokar, wanda Shugaba Joe Biden ya zartar a watan Afrilun da ya gabata, za ta dakatar da amfani da manhajar Tiktok a Amurka da dukkanin harkokin yanar gizonta matukar kamfanin Bytedance daya mallake ta bai sayarwa Amurka da jarin manhajar ba nan da ranar 19 ga watan Janairu mai kamawa.

Ku Duba Wannan Ma Amurka Na Shirin Dakatar Da TikTok

Tiktok ya bukaci a dakatar da wannan yunkuri yayin da yake kalubalantar hukuncin wata karamar kotun da ta tabbatar da dokar, da take baiwa Amurkawa kariya daga manhajojin makiya daga ketare, wacce ita ma za a iya daukaka kara a kanta zuwa kotun kolin.

Tiktok ya bukaci kotun kolin ta zatar da hukunci kan nan da 6 ga watan Janairu mai kamawa.