Mujallar Times Ta Ayyana Donald Trump A Matsayin Gwarzon Shekara A Karo Na 2

This image courtesy of TIME/TIME Person of the Year obtained on December 12, 2024 shows the cover of TIME Magazine announcing US President-elect Donald Trump as the 2024 Person of the Year.

Mujallar ta taba ayyana Trump a matsayin gwarzon shekara a shekarar 2016 bayan da ya lashe zaben shugaban Amurka.

Mujallar Times ta ayyana Donald Trump a matsayin gwarzon shekararta a karo na 2.

Mujallar ta taba ayyana Trump a matsayin gwarzon shekara a shekarar 2016 bayan da ya lashe zaben shugaban Amurka.

Al’adar mujallar ta “Gwarzon Shekara”, wacce ta samo asali a 1927, ta na la’akari da mutum ko wata fafutuka da ta yi matukar tasiri wajen sauya al’amura a shekara, ta kowane irin hali.

Sauran wadanda suka samu karramawar a baya sun hada da mai fafutuka a kan sauyin yanayi Greta Thumberg da tsohon shugaban Amurka Barack Obama da shugaban kamfanin Meta Mark Zuckerberg, da Paparoma Francis da kuma shugaban Ukraine Volodymyr Zelensky.