Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Babban Jami'in Gwamnatin Ukraine Ya Ziyarci Amurka Don Ganawa Da Tawagar Trump -  Ministan Harkokin Waje


Shugaban kasar Ukraine Volodymyr Zelenskiy
Shugaban kasar Ukraine Volodymyr Zelenskiy

Wani babban jami’in gwamnatin Ukraine ya kai ziyara Amurka domin kulla alaka da gwamnatin zababben shugaban kasa Donald Trump, wanda ya sha alwashin kawo karshen yakin Rasha a Ukraine da ya kama aiki, kamar yadda kafar yada labaran Ukraine ta ruwaito Ministan Harkokin Wajen kasar ya fada yau Laraba

Shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasar Ukraine, Andriy Yermak, ya riga ya isa Amurka, kamar yadda ministan harkokin waje Andriy Sybiha ya shaidawa manema labarai a birnin Brussels, a cewar rahoton kamfani dillancin labaran Interfax na Ukraine.

Harin da Rasha ta kai kan muhimman ababen more rayuwa a yammacin Ukraine
Harin da Rasha ta kai kan muhimman ababen more rayuwa a yammacin Ukraine

“Wannan ganawa a matakin shugaban fadar shugaban kasa nada matukar mahimmanci domin kulla alaka, da wakilan sabuwar gwamnati,” kamar yadda Interfax ta Ukraine ta ruwaito sybiha yana cewa.

Har yanzu Trump bai yi karin haske akan shirinsa na kawo karshen mamayar watanni 33 ba, saidai tsare-tsare 3 da wasu makusantansa suka gabatar na ganin burin Kyiv na zama mamba a rundunar tsaro ta NATO ba zai yiyu ba.

Zababben shugaban kasar Amurka Donald Trump
Zababben shugaban kasar Amurka Donald Trump

Haka kuma mashawartan Trump na gabatar da wasu tsare-tsare da zasu sakarwa Rasha yankuna da dama, wacce ta mamaye kaso 1 bisa 6 Ukraine.

-Reuters

Dandalin Mu Tattauna

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG