Biden Ya Gana Da Shugabannin Afirka A Angola Domin Bunkasa Aikin Jirgin Kasan Lobito

Joe Biden visita o Corredor do Lobito, em Angola 2024.

Shugaban Amurka Joe Biden ya gana da shugabannin nahiyar Afrika a tashar ruwan Lobito ta Angola a yau Laraba domin bunkasa shirinsa daka iya bude hanyar yin safarar muhimman ma’adinai daga kasashen Congo da Zambia zuwa yammacin duniya ta gabar ruwan lobito, tare da yakar kakagidan da China ta yi a yankin.

Shugabannin kasashen Angola da Congo da Zambia harma da mataimakin shugabar Tanzania sun hadu da Biden domin gudanar da taro Lobito a ranar karshe ta ziyararsa daya tilo kuma karshe a Afirka a matsayin shugaban kasa.

Biden da takwaransa na Congo Felix Tshisekedi sun jaddada aniyar bunkasa zuba jari da zaman lafiya domin baiwa kasar dake tsakiyar Afrika damar cin gajiyar dimbin arzikin ma’adinan da Allah ya bata, a cewar sanarwa da fadar White House ta fitar bayan ganawar shugabannin 2.

AFRICA-USA/

Haka kuma Biden da takwaransa na Zambia Hakainde Hichilema sun gana domin tattaunawa a kan bangaren Zambia na aikin jirgin kasan Lobito da ma wasu batutuwan.

A yadda al’amura suke, China ce babbar kasar ketare dake taka rawa a hakar ma’adinai a Jamhuriyar Dimokiradiyar Congo, inda take fitar da ma’adinan da ake ganin suna da matukar muhimmanci wajen harhada batura da wasu kayayyakin da masana’antu ke nema wajen sauyawa daga amfani da makamashin dake da nasaba da man fetur.

Biden Africa

Amurka ta ba da rancen dala miliyan 550 domin tallafawa aikin na Lobito, wanda ya kunshi yiwa layin dogon da ake da shi wanda ya karade Angola kwaskwarima tare da tsawaita shi zuwa yankin hakar ma’adinai na kasar Congo a matsayin kashin farko na aikin.

Har yanzu ba a tsayar da ranar kammala aikin ba, yayin da kashi na 2 na aikin da zai hade Lobito da Zambia ta hanyar sabon layin dogo yake matakin tsare-tsare, da nufin kafa harsashin fara shi a 2026, a cewar Washington.

Biden Africa