Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Biden Ya Bukaci Majalisa Ta Amince Da Karin Tallafin Dala Biliyan 24 Ga Ukraine


Biden
Biden

Shugaban Amurka Joe Biden ya bukaci majalisar dokokin kasar da ta amince  da karin dala biliyan 24 domin tallafa wa Ukraine da kuma kara cike ma’adanar makaman Amurka

Kamar yadda wasu jami'an Amurka biyu suka shaida wa Muryar Amurka, Shugaban ya nemi majalisar da ta amince da karin tallafawa Ukraine a yayin da gwamnatin kasar ke ci gaba da gabatar da wasu sabbin tsare-tsaren tallafi a jiya Litinin.

An yi tsare-tsaren tallafin domin fitar da wasu kudade daga cikin kudaden da majalisar ta amince da su ga Kyiv kafin Biden ya bar mulki a ranar 20 ga watan Janairun 2025.

Jami’an da suka sami ganin bukatar gwamnatin, bisa sharadin sakaya sunansu don tattaunawa da Muryar Amurka, sun bayyana cewa, sabon tallafin zai hada da dala biliyan 16 domin sake cike taskar makaman Amurka karkashin dokar ikon shugaban kasa ta Pentagon, tare da dala biliyan 8 don kera makamai a karkashin shirin tallafin tsaro na Ukraine, wanda ke mayar da hankali kan samar da bukatun tsaro na dogon lokaci ga Kyiv.

Wani jami'in tsaron Amurka ya shaidawa Muryar Amurka cewa "ko baya ga karfafawa yakin da Ukraine ke yi na tsare 'yancin ta da kuma karya lagon sojojin Rasha, haka ma tallafin kudaden zai kara karfafa shirye-shiryen sojojin Amurka ta hanyar sabunta tsari makamanta da kuma sanya hannun jari kai tsaye a bangaren masana'antar tsaro."

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG