Ana Bikin Ranar ‘Ya’ya Mata Ta Duniya

Ranar 'Ya'ya Mata

Bikin wanda ke gudana duk ranar 11 ga watan Oktoba an fara gudanar da shi ne tun cikin shekarar 2012 kuma yana maida hankali ne wajen neman kara wayar da kan al’umma “akan yadda matsalolin sauyin yanayi da tashe-tashen hankula da talauci ke shafar ‘ya’ya mata”

A yayin da ake bikin ‘ya’ya mata ta duniya, mai taken “Tunanin ‘Yan Mata Game Da Makoma,” ana sa ran gwamnatoci suyi duk mai yiyuwa wajen kiyaye makomar yara mata daga munanan abubuwan dake barazanar illata su.

Bikin wanda ke gudana duk ranar 11 ga watan Oktoba an fara gudanar da shi ne tun cikin shekarar 2012 kuma yana maida hankali ne wajen neman kara wayar da kan al’umma “akan yadda matsalolin sauyin yanayi da tashe-tashen hankula da talauci ke shafar ‘ya’ya mata” da kuma “koma bayan da ake samu akan nasarorin kare hakkin dan adam da daidaiton jinsi da aka sha wuya aka samu.”

A Najeriya da sauran kasashe da dama, har yanzu ana tauyewa ‘ya’ya mata hakkokinsu da takaita zabin da suke da shi, tare da takura makomarsu.

Suna fama da rashin damar samun ilimi da abinci mai gina jiki da hakkokin shari’a dana kiwon lafiya da kuma na kariya daga tashe-tashen hankula.

Ranar 'Ya'ya Mata

A Jamhuriyar Nijar, wata kungiyar matasa dake kula da yanar gizo INIWEB ta shirya taron baiwa yan mata horo kan yadda yakamata su rinƙa amfani da yanar giza don su anfana da ita.

Ranar 'Ya'ya Mata

Taron ya wakana ne a dakin shawara na kungiyar farar hula tournon la page a Maradi.

Ranar 'Ya'ya Mata

Yan mata da suka halarci taron sunce sun gamsu sosai da muhawarorin da aka shirya a taron.

Ranar 'Ya'ya Mata