A jamhuriyar Nijer, kungiyar FAD mai fafutukar kare hakkin mata ta kaddamar da wani zagaye a makarantun kasar, domin wayarda kan dalibai a game da wata sabuwar dokar dake haramta aurarda ‘yan mata dalibai masu shekaru 16 da haifuwa, a wani yunkurin basu damar samun ilimi mai dorewa.
A watan disambar 2017 ne shugaban kasar Nijer Mahamadou Issouhou, ya saka hannu akan wata ayar dokar, dake baiwa ‘yan mata dalibai kariya tun daga aji na daya har zuwa shekaru 16 da haifuwa matakin da tun tashin farko ya samu karbuwa a wajen ‘yan majalisar dokokin kasar.
Sakamakon lura da irin matsalolin da auren wuri ke jefa ‘yan mata cikin, sai dai kawo yanzu jama’a na jahiltar wannan dokar, hakan yasa kungiyar ONG FEMMES ACTIONS ET DEVELOPPEMENT ta shirya wannan kamfe ta wayarda kan ‘yan mata a makarantun Sakandire a daukacin kasar.
Daruruwan dalibai ne suka halarci wannan gangami domin sauraren sakonnin da kungiyar ta FAD ke tafe da su, Haoua Elhadji Abdou wata daliba a makarantar CSP Kouara ta ce taron ya fitar da ita daga jahilici.
Sai dai matashiyar tace akwai alamar tambaya a wannan tafiya, hukumomin ilimi sun yi na’am da wannan yunkuri na ONG FAD, domin a cewar Darektar bunkasa ilimin ‘yan mata Mariama Chifkao, kamfen din zai taimaka wajen wayar da kan ‘yan mata dalibai, da cewa doka ta tanadi wasu mahimman matakan dake basu kariya da dukkan wani goyon bayan da ya dace domin samun ilimi mai dorewa…
Dokar mai lamba 935 ta watan disambar 2017 da ake kira Decret Portant Sur La Protection Le Soutien Et L Accompagnement De La Jeune Fille Scolarisee a wani sashenta ta kunshi matakan yaki da miyagun malaman makarantar dake kwatanta amfani da matsayinsu don tafka ta’asa, akan dalibansu ‘yan mata saboda haka gangamin na ONG FAD bai manta da wannan batu ba.
Wakilin Muryar Amurka a Yamai Sule Mumuni Barma ya aiko mana karin bayani.
Facebook Forum