Gwamnatin Najeriya Na Shirin Janye Harajin VAT Kan Magunguna

Kungiyar Kula Da Lafiyar Mata Da Kananan Yara Ta Bada Tallafin Magunguna Da Kayayyakin Aiki A Jihar Kano

A jiya Laraba, gwamnatin Najeriya ta bayyana cewa ta kammala aiki a kan dokar ofishin shugaban kasa ta janye harajin sayen kaya (VAT) a kan magunguna da na’urorin kiwon lafiya.

Da yake bayyana hakan a cikin wata sanarwa, mai magana da yawun ma’aikatar lafiya da walwalar jama’a, Alaba Balogun, yace an kammala aikin daidaita yadda za’a aiwatar da dokar yanzu saura a wallafata.

“Gaba mafi mahimmanci a dokar ita ce tabbatar da cewa hukumar tattara haraji ta Najeriya (FIRS) da takwararta ta yaki da fasa kwabri na iya fara aiwatar da shirin daina cazar harajin VAT a kan magunguna da na’urorin kiwon lafiya,” a cewarsa.

A cewar sanarwar, wallafa dokar da aka hade hancin bangarorinta na nufin cimma daya daga cikin manufofin ma’aikatar, na sakarwa harkar kiwon lafiya mara.