Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ana Gudanar Da Zaben Kananan Hukumomi A Jihar Filato


Wata rumfar zabe a jihar Sokoto
Wata rumfar zabe a jihar Sokoto

Hukumar zaben jihar filato ta bayyana cewar mutane 75 ne ke takarar neman kujerun ciyamomi, a yayin da 788 ke fafatawa wajen neman kujerun kansiloli a mazabu 355.

Jam’iyyu 11 ne ke fafatawa a zaben kananan hukumomin jihar Filato 17, domin zaben ciyamomi da kansilolin da zasu ja ragamar al’amuransu nan da shekaru 2 masu zuwa.

Hukumar zaben jihar filato ta bayyana cewar mutane 75 ne ke takarar neman kujerun ciyamomi, a yayin da 788 ke fafatawa wajen neman kujerun kansiloli a mazabu 355.

Hukumar zaben jihar ta bullo da wani tsarin tantance masu kada kuri’a bata hanyar amfani da na’ura ba a rumfunan zabe 4, 989, domin kara armashin zaben kananan hukumomin.

Shugaban hukumar zaben jihar Filato, Daniel Cishak, ya jaddada aniyar hukumar na gudanar da sahihin zabe cikin adalci.

Gwamna Caleb Mutfwang ne ya rushe tsaffin zabubbub ciyamomi da kansiloli sa’ilin daya karbi ragamar mulkin jihar, sannan ya rantsar da kantomomin riko a ranar 10 ga watan Yunin 2023.

A ranar 7 ga watan Satumbar da ya gabata, aka sauke kantomomin sannan daraktocin gudanarwa suka karbe ragamar kananan hukumomin domin share fagen gudanar da zaben.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG