Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

JOHESU Ta Bada Wa’adin Kwanaki 15 Gabanin Shiga Yajin Aiki Akan Bukatunta

JOHESU ta tsunduma cikin yajin aiki tsakanin ranar 19 ga watan Mayu zuwa 6 ga watan Yunin bara (2023), makonni 2 da suka kusan durkusar da harkar jinya a asibitocin gwamnati.

Ma’aikatan jinyar dake aiki a asibitocin gwamnati karkashin inuwar gamayyar kungiyoyin ma’aikatan kiwon lafiya (JOHESU) sun baiwa gwamnatin tarayyar Najeriya wa’adin kwanaki 15 ta warware dukkanin batutuwan dake tsakaninsu ko kuma su tsunduma cikin wani sabon yajin aiki.

Sanarwar dake dauke da sa hannun shugaba da sakataren JOHESU na kasa, ta bayyana cewar gwamnatin tarayyar ta gaza biyan bukatun kungiyar tun daga watan Yulin bara lokacin da suka jingine yajin aikin, sakamakon alkawarin da Shugaban Kasa Bola Tinubu ya dauka na sa baki a lamarin.

JOHESU ta tsunduma cikin yajin aiki tsakanin ranar 19 ga watan Mayu zuwa 6 ga watan Yunin bara (2023), makonni 2 da suka kusan durkusar da harkar jinya a asibitocin gwamnati.

An janye yajin aikin sakamakon alkawarin da Tinubu ya yi na shiga tsakani.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG