A jiya Talata, ministan babban birnin tarayyar Najeriya, Abuja, Nyesom Wike, ya bayyana cewar baya nadamar yakar jam’iyyar PDP da ya yi a zaben shugaban kasar 2023.
Wike, wanda ya bayyana hakan a cikin shirin siyasar tashar talabijin ta Channels mai taken “Politics Today”, ya musanta zargin sabawa dokokin jam’iyyar saboda kin taimakawa Atiku Abubakar, dan takarar shugaban kasar da PDP ta tsayar a zaben.
Ya kare matsayarsa, inda yace ya yanke shawarar yin hakan ne saboda tabbatar da gaskiya da adalci.
A kakar zaben 2023, Wike, sa’ilin yana kan kujerar gwamnan jihar Ribas, ya hada kai da wasu gwamnonin PDP 4 da aka sabawa, da suka hada da Samuel Ortom na jihar Benuwe da Seyi Makinde na jihar Oyo da Okezie Ikpeazu na Abiya da kuma Ifeanyi Ugwuanyi na jihar Enugu domin yakar takarar Atiku.
Gwamnonin 5 sun dage akan matsayarsu ta sai an sauke Sanata Iyorchia ayu daga kan kujerar shugabancin jam’iyyar PDP na kasa a matsayin sharadin marawa takarar Atiku Abubakar, dake rike da tutar takarar jam’iyyar baya.
A karshe dai Atiku yayi rashin nasara a zaben shugaban kasar a hannun Bola Tinubu, dan takarar jam’iyyar APC, wanda a karkashin gwamnatinsa Wike ke rike da mukamin minista.
Dandalin Mu Tattauna