Kasa da sa’o’i 24 da Labarin yiyuwar karin farashi a kan kowacce litar mai a kasar, ’yan Najeriya sun shiga rudani sakamakon yadda lamarin ya tabbata ta bakin kungiyar dilalan mai na IPMAN, inda gidajen mai na ‘yan kasauwa ke sayar da litar mai sama da dubu 1 da 100, kuma masana ke ce cewa hakan zai kara ta’azzara talauci a tsakanin ‘yan kasar muddin ba’a dauki matakan da suka dace a kan lokaci ba.
Kafin sanarwar karin farashi a yau dai ana sayar da kowacce litar mai a kan Naira 897 a gidajen man NNPC a Abuja, babban birnin kasar, sannan gidajen man ‘yan kasuwa ke sayarwa daga naira dubu 1 da 100 lamarin da a yanzu ake sayarwa a NNPC kan Naira dubu 1 da 30 kamar yadda wata da ta sha man a yau wacce ta bukaci a sakaya sunanta ta shaida mana.
Da muka tuntubi shugaban kungiyar dilallan man fetur na Najeriya, Alhaji Maigandi Shattima, ya ce tabbas an yi kari a farashin litar mai, sai dai ya bukaci ‘yan kasa su kwantar da hankulan suna daukan matakan saukakawa al’umma a yanayin da ake ciki.
Tuni dai ‘yan kasa suka fara tofa albarkacin bakinsu ga wannan karin inda, Mallam Aminu Abbas Gumel, ya ce karin ya kara jefa mutane cikin rudani ne kawai.
A yayin da ‘yan Najeriya ke ci gaba da kokawa a game da wannan sabon matakin kara farashi, masani a fannin albarkatun man fetur, Dakta Ahmad, Adamu ya ce mafita ga matsalar tsadar mai shi ne ‘yan kasa su rungumi sabon tsari na makamashin iskar gas da tsarin amfani da tsarin mota na al’umma ba na kai ba.
A wani bangare kuma, majiyoyi daga kamfanin NNPCL sun yi nuni da cewa kamfanin ya bude kofa ga dukkan ‘yan kasuwa su rika zuwa matatar man fetur na Dangote kai tsaye su sayi mai, kuma An rufe babin biyan rarar da kamfanin ya saba biya.
Alkaluma daga bakin ‘yan kasa da suka bukaci a sakayya sunansu sun yi nuni da cewa, karin farashin kowacce litar mai na yau ya kawo sauyi a farashin kayayyakin masaraufi kai tsaye a kasuwanni kamar na Wuse inda wasu ‘yan kasuwa suka canja farashin kaya da kaso 30 cikin 100.
A saurari cikakken rahoton Halima Abdulra'uf