A jiya Talata, kungiyar yaki da cutar sankara ta duniya ta sanar da zaben Dr. Zainab Shinkafi-Bagudu a matsayin zababbiyar shugabanta a wa’adin shekaru 2 daga 2024 zuwa 2026.
Haka kuma kungiyar ta sanar da zaben sabuwar majalisar daraktocinta mai mambobi 14, sakamakon babban taronta daya gudana ta na’ura a ranar 8 ga watan Oktoban da muke ciki.
Sanarwar da kungiyar ta fitar tace ilahirin mambobinta dake fadin duniya suka taka rawa a zaben, inda ta sake jaddada aniyarta ta hade kan masu ruwa da tsaki a yaki da cutar sankara a fadin duniya.
Dr. Zainab wacce ta fito daga Najeriya ta kasance ‘yar Afrika ta farko da aka zaba a wannan mukami. ita ce ta assasa gidauniyar yaki da cutar sankara ta “Medicaid Cancer Foundation kuma kwararriyar likitar yara ce sannan mamba ce a kungiyar yaki da cutar sankara ta Najeriya wato Nigerian Cancer Society da takwararta ta Amurka American Society for Clinical Oncology.