Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Najeriya Ta Samu Karin Dala 1.8m Domin Tallafawa Mutanen Da Ambaliyar Ruwa Ta Shafa

Wasu mazauna Maiduguri suna yin kaura bayan da ambaliyar ruwa ta mamaye unguwanninsu (Hoto: Facebook/NEMA)
Wasu mazauna Maiduguri suna yin kaura bayan da ambaliyar ruwa ta mamaye unguwanninsu (Hoto: Facebook/NEMA)

Kudaden zasu baiwa kungiyoyi masu zaman kansu na Najeriya dana kasa da kasa damar samar da agajin gaggawa ga fiye da mutane 180, 000 a jihohin Borno, Benuwe, Adamawa da Yobe.

Hukumar kula da masu kaura ta duniya (IOM) ta saki fiye da dala miliyan 1.8 da nufin magance muhimman bukatun mutanen da ambaliyar ruwa ta shafa a fadin najeriya.

Kudaden zasu baiwa kungiyoyi masu zaman kansu na Najeriya dana kasa da kasa damar samar da agajin gaggawa ga fiye da mutane 180, 000 a jihohin Borno, Benuwe, Adamawa da Yobe.

Agajin, da aka bayar ta asusun bada agajin gaggawa zai kunshi samarda wuraren zama da tallafin da bai shafi abinci ba da taimakon kudade da bada kariya da ruwan sha da tabbatar da tsafta domin ragewa mutanen matsalolin da suka fi damunsu tare da dawo dasu cikin hayyacinsu da gaggawa.

Kudaden da suka zamo kari akan wadanda aka ware a babban asusun bada agajin gaggawa da asusun bada agaji na Najeriya, zasu taimaka wajen karfafa ayyukan bada kariya ciki harda ayyukan bada kariya ga kananan yara da mata a matakin unguwanni da kuma na dakile matsalar cin zarafi mai nasaba da jinsi a wasu daga cikin wuraren da ake sa ido akai.

A bana ambaliyar ruwa ta shafi fiye da mutane milyan 1.2 a fadin Najeriya, galibinsu a jihar Borno wacce ta kasance wurin da matsalolin bada agaji suka yi katutu.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG