Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Najeriya Ta Kaddamar Da Yaki Da Cutar Kwalara


FILE - Ambaliyar ruwa a jihar Borno
FILE - Ambaliyar ruwa a jihar Borno

Cibiyar yaki da cututtuka ta Najeriya CDC, ta ce cutar kwalara da mace-mace sun karu da fiye da kashi 200 a bana idan aka kwatanta da na bara.

Hukumar kula da cututtuka ta Najeriya CDC ta fada cikin rahoton da ta fitar na wannan mako kan annobar cutar kwalara a kasar, cewa ta samu kusan mutane 11,000 da suka kamu da cutar a bana, wanda ya karu da kashi 220 cikin dari idan aka kwatanta da na shekarar 2023.

Rahoton ya ce adadin wadanda suka mutu a cikin wadannan lokutan ya karu daga 106 zuwa 359.

Hukumar CDC ta ce jihar Legas ce ke da kashi 43 cikin 100 na masu dauke da cutar a kasar, yayin da wasu jihohi kamar Kano da Katsina da Jigawa da kuma Borno ke samun adadi mai yawa.

A watan da ya gabata, ambaliyar ruwa mafi muni cikin shekaru 30 da suka gabata ta yi barna a jihar Borno mai fama da tashe-tashen hankula, lamarin da ya kara ta’azzara matsalar jin kai a can. Dubban mutane sun rasa matsugunansu kuma sun koma sansanoni masu cunkoso.

Kwamishinan lafiya na jihar Borno Baba Mallam Gana, ya ce yanzu suna fuskantar babban kalubalen kiwon lafiyar jama'a, wanda ke bukatar kulawar gaggawa da daukar mataki.

Ya kara da cewa ambaliyar ta haifar yanayi na yaduwar cututtuka kamar kwalara ta hanyar gurbata hanyoyin ruwa da kuma rushe tsarin tsaftar muhalli.

Kwalara wasu kwayoyin cuta ne da yawanci ke yaduwa ta hanyar gurbataccen abinci ko ruwan sha, wadda ke haifar da gudawa mai tsanani da tsotse ruwan jikin dan adam.

Hukumar Yaki da Cututtuka Masu Yaduwa ta Najeriya CDC ta kaddamar da shirin bayar da agajin gaggawa na kasa tare da hadin gwiwar hukumomin jihohi a kokarin dakile cutar.

Ma'aikatar lafiya ta Najeriya ta aika da alluran rigakafin kwalara zuwa yankunan da abin ya shafa don taimakawa wajen rage illar cutar.

Jihar Borno kadai ta sami allurai 300,000 kuma hukumomin jihar sun ce an raba su ga sansanonin wadanda ambaliyar ruwa ta raba da muhallansu.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG