Kudin shigar gwamnatin Najeriya daga masu zuba jari na ketare ya ragu zuwa dala miliyan 29.63 a zango na 2 na shekarar 2024.
Rahoton baya-baya nan a kan jarin daya shigo Najeriya da hukumar kididdigar kasar (NBS) ta fitar ya nuna cewa jarin ketaren ya ragu da kaso 65.33 cikin 100 idan aka kwatanta da dala miliyan 86.03 da aka samu a irin wannan lokaci a bara.
Hakan ya kasance maki mafi kankanta da aka samu tun cikin shekarar 2013 a bisa bayanan da ake dasu.
Yawan jarin ya kuma sauka da kaso 74.97 cikin 100 daga dala milyan 119.18 da aka bada rahoton samu a zangon farko na shekarar 2024 da muke ciki.
Alkaluman da NBS ta fitar sun nuna cewa kudin shigar Najeriya na ketaren sun hada har da basussuka da sauran kadarori.
Galibin kudin shigar da Najeriya ta samu a zangon na 2 na 2024 sun zo ne daga basussukan da ta ciyo, da suka kai dala miliyan 29.82.
Dandalin Mu Tattauna