Gwamnan bankin CBN, Olayemi Cardoso ya bayyana karin kudin ruwan ne bayan taron kwamitin manufofin kudin bankin karo na 296 da aka gudanar a birnin Abuja. Bankin CBN na ganin nan da dan lokaci ‘yan kasa zasu ga fa’idar matakin da ya dauka.
A bisa wannan matakin da bankin CBN ya dauka, Muryar Amurka ta nemi jin ta bakin wasu masu gasa masara a kan titunan Abuja inda wani ya ce an sami dan sauki a samun masara saboda damina wata kuma ta ce atile da take saya a kan dubu 20 kowanne buhu ya koma dubu 30.
Kwamitin manufofin kudin CBN din dai ya bada dalilan da ya sanya aka dauki matakin kara kudin ruwan da maki 50. A bayaninta, jagorar sashen manufofin kudin CBN, Dakta Ladi Raulatu Bala-Keffi MNI, ta ce an dauki matakin ne don kawo sauki ga hauhawar farashin kayayyaki ta hanyar rage yawan kudadden dake yawo a cikin kasa.
A wani bangare kuma, Dakta Raulatu ta yi karin Haske a kan batun maido da kudadden da aka dade ba’a yi amfani da su a asusun ba a bankunan kasuwanci zuwa babban bankin kasar don kar batagari su sami damar wawushe su ko kuma bankunan kasuwancin su ci gaba da juya su suna samun riba ba tare da cin moriyar masu asusun ba.
Najeriya dai na fama da matsalolin matsin tattalin arziki mafi muni a baya-bayan nan wanda ya yi sanadiyar tsadar rayuwa, makamashi, da masana tattali arziki suke cewa baya rasa nasaba da manufofin gwamnati kama daga cire tallafin man fetur a watan Mayun shekarar 2023 da tsarin canjin kudi na bai daya da aka bijiro da shi watannin kadan bayan karbar rantsuwar kama aikin shugaba Bola Tinubu
Saurari cikakken rahoton:
Your browser doesn’t support HTML5