WASHINGTON, D. C. - A karkashin sabbin sharuddan, wajibi ne bankuna da suke da sahalewar yin hada-hadar kudi ta kasa da kasa su kasance su na da jarin akalla naira biliyan 500. A halin yanzu, wajibi ne fiye da bankuna 20 a kasar su tanadi karin jari cikin shekaru biyu domin cika sharadin babban bankin kasar.
“Bankunanmu sun fara gabatar da shirye-shiryen cika sabbin sharuddan kara yawan jarin hada-hadarsu daidai da umurnin babban bankin Najeriya”, acewar kakakin babban bankin na Najeriya, Hakama Sidi Ali.
"A yanzu haka babban bankin ya na duba shirye-shiryen na su”, Hakama ya kara da cewa.
Babban bankin kasar ya ce masu ba da lamuni na bukatar karin kudade musamman bayan da aka rage darajar kudin kasar a hukumance sau biyu tun daga watan Yunin bara.
Hauhawar farashin kayayyaki da ƙarancin ci gaban tattalin arziki na tsawon shekaru goma da kuma wasu matakan da gwamnati ke ɗauka don haɓaka tattalin arziki sun haifar da tashin farashin kayayyaki da kuma ta'azzara tsadar rayuwa.
-Reuters
Dandalin Mu Tattauna