Babban Limamin Masallacin Jos Ya Rasu

Sheikh Muhammad Lawal Adam

Wata sanarwa daga sakataren yada labarai na kungiyar JNI a jihar Filato, Sani Mudi, yace Sheihk Muhammad Lawal Adam ya rasu yana da shekaru tamanin a duniya.

Allah ya yi wa babban limamin masallacin Jos ta tsakiya Sheikh Muhammad Lawal Adam rasuwa a yammacin yau, Alhamis, 11 ga Yulin 2024, bayan gajeruwar rashin lafiya.

Wata sanarwa daga sakataren yada labarai na kungiyar JNI a jihar Filato, Sani Mudi, yace Sheihk Muhammad Lawal Adam ya rasu yana da shekaru tamanin a duniya.

Sanarwar tace malami ne kwararre, masanin shari'a na Musulunci, sanannen mai tafsiri na Alkur'ani mai girma kuma jagoran al'ummar Musulmi.

An nada shi mataimakin babban Limamin a shekara ta 2009 sannan kuma aka nada shi Babban Limamin a shekarar 2015.

Za a yi jana’izarsa gobe Jumma'a 12 ga Yulin da muke ciki da safe bayan sallar jana’iza.

Al"ummar Musulmin Jos sun yi matukar kewar wannan malami da ake girmamawa.