Hakan abinda ke bayyana aniyarta ta yin adawa da kokarin daukaka alaka ne tsakanin kasashen mambobin NATO da kasashen nahiyar Asiya irinsu Japan da Koriya ta Kudu da kuma Philipines.
Sanarwar da mai magana da yawun ma’aikatar wajen kasar ya fitar na zuwa kwana guda bayan da NATO ta bayyana China da “babbar mai tallafawa Rasha” a yakin da take yi da Ukraine.
A cewar kakakin gwamnatin China, Lin Jian, yayin a jawabinsa na yau da kullum, “babu hankali a batun yiwa China kage da NATO ke yi game da daukar nauyin yakin Ukraine kuma akwai wata mummunar manufa akan hakan.” inda ya jaddada cewar China na da matsaya mai ciki da adalci akan batun Ukraine.
China ta bata da Amurka da kawayenta na Turai akan yakin Ukraine, inda ta ki yin allawadai da mamayar da Rasha ke yi koma ta kira abinda takalar fada don gudun kar ta sabawa mahukuntan birnin moscow. tun bayan mamayar rashar, cinikayyar dake tsakanin kasashen 2 ta karu, akalla ta rage tasirin jerin takunkuman da kasashen yammacin duniya suka kakaba mata.
A sanarwar da ta fitar yayin wani taron koli a birnin Washington, NATO tace China ta zamo mai tallafawa yakin ta hanyar “alaka marar kaidi” dake tsakaninta da Rasha da kuma gagarumin goyon bayan da take baiwa kamfanonin makaman Rasha.
Lin ya kara da cewa alakar cinikayyar dake tsakanin China da Rasha halastacciya ce kuma wacce hankali ya yarda da ita a bisa dacewa da ka’idojin Hukumar Cinikayya ta Duniya (WTO).
Ya cigaba da cewa abinda ake kira da tsaron kungiyar NATO barazna ne da tsaron sauran kasashe. China na goyon bayan matsayar Rasha na cewar fadadar NATO barazana ce ga Rasha, wacce hare-haren da take kaiwa Ukraine basu yi komai in banda kara karfafa kawancen, abinda ya sabbaba kasashen Sweden da Finland zama mambobin kungiyar a hukumance.
-AP
Dandalin Mu Tattauna