Shugaban Kungiyoyin Amnesty da Transperency International har da CISLAC masu sa ido a harkokin gudanar da Majalisa Auwal Musa Rafsanjaniya ce abu ne mai wuya Najeriya ta dakatar da yarjejeniyar SAMOA.
Rafsanjani yace Najeriya ta ratabba hannu ne domin abubuwa biyu, “na farko tana nema a yi da ita a kasashen duniya tunda a yanzu ta zama saniyar ware, babu wanda yake mutunta kasar a waje, abu na biyu kuma tana bukatar kudi domin ta riga ta ci basussuka da suka yi mata katutu, saboda haka ba za ta janye ba”.
Amma yace akwai dama da ake bayarwa a ko wacce yarjejeniya in wata kasa tana so ta fita, za ta iya fita.
Sai dai da yake zantawa da Muryar Amurka, Dan Majalisa mai wakiltan Yamaltu Deba daga Jihar Gombe, Inuwa Garba yace Majalisa ba za ta lamunta ba.
Inuwa ya ce ba a bi tsari wajen sa hannu a yarjejeniyar ba, domin kundin tsarin mulkin Najeriya ya tanada cewa ba za a yi amfani da wata yarjejeniya ba sai an kawo ta Majalisa an amince da ita tukuna, kuma ba a kawo wannan ba.
Inuwa ya ce a irin wannan yarjejeniya akwai yankin da ke bada dama a janye, saboda haka Majalisa ta bada shawarar a janye daga wannan yarjejeniya domin an yi cushe a cikin dokokin ta, kuma haka ya saba wa kundin starin mulkin kasa, da kuma tsarin adinai da al'adun kasar.
Shi ma dan Majalisa daga jihar Jigawa, Makki Abubakar Yalleman ya kara jadadda wanan batu inda ya baiyana ra'ayin sa yana cewa ‘yan Majalisa wai wai suka rika jin labarin yarjejeniyar, domin ba wanda ya kawo batun yarjejeniyar a gaban Majalisa balle ya nemi izini, kamar yadda Kundin Tsarin Mulkin kasa ya tanada, saboda haka Majalisa ta ce a je a yi bincike sosai kan wannan yarjejeniya kafin a sahale wa wadanda suka sa hannu.
Sakamakon gabatar da kudirin gaggawa mai matukar mahimmanci ga kasa da wasu ‘yan majalisa 88 suka yi, Majalisar Wakilai ta bukaci gwamnatin Najeriya ta dakatar da aiwatar da yarjejeniyar SAMOA mai cike da cece-kuce har sai an kammala fayyacewa tare da warware dukkanin wadansu kulle-kulle dake cikinta.
A yayin gabatar da kudirin a ranar Talata, wani dan majalisa, Aliyu Madaki, ya ja hankalin majalisar ga wata shedarar yarjejeniyar da ta yi bayani akan daidaiton jinsi wacce ya bayyana da tarkon daka iya yin illa ga tarbiya a Najeriya.
Wannan shi ne karo na farko da Majalisa da ke da Jamiyyu daban daban har 8, ta hada kai, ta yi magana da murya daya kan wani abu da ya saba da ra'ayin mafi yawan al'ummar kasar.
A saurari rahoton Medina Dauda:
Your browser doesn’t support HTML5