Sakamakon gabatar da kudirin gaggawa mai matukar mahimmanci ga kasa da wasu ‘yan majalisa 88 suka yi, Majalisar Wakilai ta bukaci gwamnatin Najeriya ta dakatar da aiwatar da yarjejeniyar SAMOA mai cike da cece-kuce har sai an kammala fayyacewa tare da warware dukkanin wadansu kulle-kulle dake cikinta.
A yayin gabatar da kudirin a yau Talata, wani dan majalisa, Aliyu Madaki, ya ja hankalin majalisar ga wata shedarar yarjejeniyar da ta yi bayani akan daidaiton jinsi wacce ya bayyana da tarkon daka iya yin illa ga tarbiya a Najeriya.
Haka kuma majalisar ta umarci kwamitocin da al’amarin ya shafa su gudanar da bincike game da tanade-tanaden yarjejeniyar masu cike da cece-kuce.
Yarjejeniyar da gwamnatin tarayya ta rattabawa hannu tsakaninta da tarayyar Turai ta yamutsa hazo, inda akasarin al’umma suka yi tir da abinda suke yiwa kallon amincewa ne da hakkokin ‘yan luwadi da madigo da sauran marasa tarbiya da Najeriya tayi.
A yayin wani taron manema labarai a Asabar din data gabata, Ministan Kasafi da Tsare-Tsaren Tattalin Arziki, Atiku Bagudu, da takwaransa na Yada Labarai, Muhammad Idris, sun ce babu yadda za’a yi Najeriya ta kulla yarjejeniyar da ta ci karo da tanade-tanaden kundin tsarin mulkinta.
A cewar Bagudu, dalilan da suka sabbaba Najeriya shiga yarjejeniyar sun hada da bukatar bunkasa samun wadatar abinci da cigaban tattalin arzikinta.
Dandalin Mu Tattauna