Yayin wani taron manema labarai da su ka gudanar a babban birnin tarayya Abuja, Ministan Watsa Labaran Najeriya Mohammed Idris da takwaran sa na Ma'aikatar Kasafin Kudi da Tsare-tsare Abubakar Bagudu sun musanta zargin da ake yi na batun LGBTQ da kudi a yarjejeniya ta SAMOA.
Ganin yadda batun yarjejeniyar SAMOA ke ci gaba da janyo martani mai zafi a tsakanin 'yan Najeriya duk da cewa gwamnati ta musanta zargin yunkurin kawo auren jinsi guda a kasar, yanzu gwamnatin Najeriya ta ce za ta maka gidan jaridar Daily Trust da ya buga labarin tun farko a gaban kuliya.
Ministan yada labarai da wayar da kan al'umma Mohammed Idris Malagi ya yi karin haske cewa gwamnati za ta dauki mataki akan jaridar.
Ya ce za mu kai kara, saboda shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ba zai yarda ya dauki irin wannan mataki ba, ba kuma zai yarda wani wakilin sa ya sa hannu a wata yarjejeniya da zata saba wa dokokin kasa da dokokin addinan mu ba.
Ya kara da cewa “Wanan labari karya ne babu shi, ba a yi ba, babu shi. Gwamnati za ta shigar da kara domin neman hakkin ta.”
Shi kuwa ministan kasafin kudi da tsare-tsare, Abubakar Atiku Bagudu, ya ce baya ga babu batun auren jinsi, batun kudi ma bai zo da sharadi a cikin yarjejeniyar ba.
Bagudu ya ce ma'aikatar sa ce aka dora wa alhakin sa hannu a wannan yarjejeniya kuma ba ita ce ta farko ba. Akwai yarjejeniyar Kotono wacce kasashen EU da OACPS suka sa hannu kafin wannan, kuma ana amfana ne ta hanyoyin gudanarwa, da ilimin zamani na kimiyya da fasaha, kiwon lafiya da makamantan su.
“Sharri ne kawai domin babu inda aka bada kudi ko kuma a sabawa dokokin kasa, in ji Bagudu.
A nata bangaren, shugabar Gidauniyar Mata ta Tozali, Maimuna Yaya Abubakar, ta ce gwamnati ta koma a sake duba wannan yarjejeniyar, saboda ba za ta dauki batun son kudi ta sa a gaba sannan ta saba wa dokokin kasar ba.
Maimuna ta ce akwai sharuda da ake bi kafin a kai ga sa hannu a irin wadannan yarjejeniyoyin, saboda haka ta fi ganin a soke yarjejeniyar baki daya, a samu a warware matsalar kafin a sake sa hannu.
Sai dai duk kokarin samun martani daga jaridar Daily Trust da ta buga labarin tun farko, amma kokari ya ci tura.
Saurari cikakken rahoton Medina Dauda:
Dandalin Mu Tattauna