Mambobin Kungiyar Manyan Malaman Jami’o’in Najeriya (SSANU) da takwarorin na Ma’aiktan Da Ba Malamai Ba (NASU) sun gudanar da zanga-zanga a harabar jami’o’in dake fadin Najeriya a yau Talata domin neman a biyasu kudaden albashin da suke bi bashi.
Fusatattun ma’aikatan na dauke da kwalaye masu dauke da mabambantan sakonni a sa’ilin da suke gudanar da maci a cikin harabar jami’o’in, inda suke kira ga gwamnatin tarayya ta sakar musu albashin da ta rike musu tare da aiwatar da sauran bukatunsu.
Members of the Senior Staff Association of Nigerian Universities (SSANU) of Ahmadu Bello University have also staged a peaceful protest within the campus to demand the immediate release of their withheld salaries.#CTVTweets pic.twitter.com/6qXajA1GfR
— Channels Television (@channelstv) July 9, 2024