Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

SSANU Da NASU Zasu Fara Yajin Aikin Gargadi A Ranar 18 Ga Watan Maris


SSANU/NASU
SSANU/NASU

Kungiyar Manyan Ma'aikatan Jami'o'in Najeriya (SSANU) da takwararta ta Ma'aikatan Jami'ar da ba Malamai Ba (NASU) sun ayyana shiga yajin aikin gargadi na kwanaki 7 tun daga ranar 18 ga watan Maris din da muke ciki.

WASHINGTON DC - A cewarsu, zasu yi hakan ne domin yin matsin lamba ga gwamnati ta biya albashin watanni 4 data rikewa mambobinsu sakamakon yajin aikin gamagarin da suka shiga a shekarar 2022.

Shiga yajin aikin na daga cikin shawarwarin da kwamitin hadin gwiwa na kungiyoyin 2 ya cimma, bayan wani taro daya gudanar a birnin Akuren jihar Ondo a karshen makon daya wuce.

Shugaban kungiyar ssanu, muhammad ibrahim, wanda ya karantawa manema labarai sanarwar bayan taro a abuja a yau litinin, an yanke shawarar shiga yajin aikin ne a matsayin matakin karshe kasancewar takardun korafe-korafe da sauran sakonni tsakaninsu da gwamnatin tarayya basu samar da kyakkyawan sakamako akan bukatar biyan albashin da aka rike musu ba.

A cewar sanarwar, "matukar gwamnatin tarayya ta kasa daukar matakin warware wannan matsala tare da yin martani ga sakonnin da muka aike mata, ya zama wajibi mambobin kungiyoyin 2 su gudanar da ganawar gaggawa domin daukar tsauraran matakan da doka ta aninta dasu domin warware matsalar.

Al'amarin na zuwa ne a daidai lokacin da kungiyoyin ke zargin gwamnatin tarayya da yiwa batun mambobinsu rikon sakainar kashi.

Shugaban Kasa Bola Tinubu ya bada umarnin biyan ma'aikatan jami'o'i albashin da aka rike musu sakamakon yajin aikin da suka yi a shekarar 2022.

Saidai gamayyar kungiyoyin ASUU da NASU harma da takwararsu ta ma'aikatan dake fannin kirkire-kirkire suka yi ikirarin cewar har yanzu basu ga albashin da aka rike musun ba tare da bada wa'adin mako guda makonni 2 da suka gabata.

SSANU da NASU sun ce sun yi dukkanin mai yiyuwa domin hana mambobinsu shiga yajin aikin da nufin ci gaba da samun wanzuwar zaman lafiya da daidaituwar al'amura.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG