Kungiyar ma'aikatan Jami'o'i tare da hadin gwiwa kungiyoyin manyan ma'aikatan jami'o'i SSANU, da kuma kungiyar JAC kungiyar da ba na ilimi ba, sun dau matakin fara zanga-zangar lumana, don nuna rashin gamsuwar su da wasu abubuwa guda 8.
Kamar yadda shugaban kungiyar NASU na Jami'ar Kimiyya da Fasaha ta Wudil a jihar Kano, Nura Mohammed ya zayyana, sun shiga yarjejeniya da Gwamnatin tarayya tun a shekarar 2009, wadanda su ka hada da rashin dai-daiton biyan kudin albashi na IPPIS, da batun biyan kudin alawus-alawus na ma'aikatan.
Kana da bashin da ma'aikatan ke bi na karin albashi da gwamnati ta yi, akwai batun sabunta yarjejeniyar da gwamnati ba ta yi ba bayan shekara biyar.
Haka sai batun fansho na ma'aikata da suka bar aiki, kana da yadda ba'a kula da Jami'o'i mallakar Jihohi, da bukatar kafa kwamiti na musamman da zai rika ziyarar ganin ayyukan jami'o'i da gwamnati ba ta yi, inda ya ce yin haka ba dai-dai ba ne. Wadannan da ma wasu dalilai ne suka sa su daukar wannan matakin.
Nura Mohammed, ya ce gwamnati ta na fifita kungiyar Malaman Jami'o'i akan ma'aikatan jami'o'in, saboda haka suna neman a dai-daita sahu.
Shi kuwa wani Malami a tsangayar Ilimi ta Jami'ar Abuja Dr. Usman Abdullahi Manu, ya yi bayanin cewa, idan har wadannan ma'aikatan suka shiga yajin aiki, to fa zai shafi Malaman Jami'o'in sossai, domin su ne masu ayyukan shirya albashin Malaman da sauran ayyukan gudanar da jami'o'in.
Dr. Manu yana mai ba gwamnati shawarar cewa, ta yi maza ta taimaka wa bangaren ilimi, idan ana so kasa ta ginu saboda ilimi shi ne ginshinkin cigaba a ko ina cikin duniya.
Ga rahoton Medina Dauda ta hada a cikin sauti.