Gwamnati Ta Yi Wa Hadakar Kungiyar Kwadago Tayin Dubu 62 A Matsayin Albashi Mafi Karanci

Shugaban Najeriya, Bola Tinubu, a ranar Ma'aikata ta Duniya

Hakan ya biyo bayan komawa kan teburin tattaunawa ranar Laraba bayan kungiyoyin, a ranar Talata, suka jingine yajin aikin da suka tsunduma ranar Litinin da ya gabata.

Duk da koken Kungiyar Gwamnonin Najeriya cewa biyan dubu 60 a matsayin mafi karancin albashi ba zai yiyu ba, gwamnatin tarayya ta yi wa kungiyoyin kwadago ta TUC da NLC tayin dubu 62 a matsayin albashi mafi karanci.

Hakan ya biyo bayan komawa kan teburin tattaunawa ranar Laraba bayan kungiyoyin, a ranar Talata, suka jingine yajin aikin da suka tsunduma ranar Litinin, 3 ga watan Yuni da muke ciki.

Ku Duba Wannan Ma Ba Za Mu Iya Biyan Mafi Karancin Albashin Naira Dubu 60 Ba-Gwamnoni
Ku Duba Wannan Ma MAFI KARANCIN ALBASHI: Babu Wani Abun Fargaba – Wale Edun

Sai dai a nata bangaren, kungiyar kwadagon ta rage kudin da ta ke bukata gwamnati ta biya a matsayain albashi mafi kankanta daga naira dubu 494 zuwa dubu 250.

A ranar Talata ne kungiyoyin suka janye yajin aiki na mako guda domin neman a cimma matsaya kan nawa gwamnati zata biya a matsayin albashi mafi karanci a kasar.

Kawo yanzu, an kammala tattaunawar ba tare da an cimma matsaya ba, sai dai sun yi alkawarin dawowa kan teburi domin samun mafita.

Gwamnatin tarayya tayi alkawarin biyan mafi karancin albashin daya zarta dubu 60 bayan da suka koma kan teburin tattaunawa.