Gwamnonin jihohin Najeriya sun roki mambobin kwamitin nan mai bangarori 3 ya amince da mafi karancin albashin da zai zama mai adalci da dorewa.
Gwamnoni 36 dake cikin Kungiyar Gwamnonin Najeriya sun ce tayin Naira dubu 60 da gwamnatin tarayya ta yi ba abune mai dorewa ba kuma ma ba zai yiyu ba.
Sanarwar da mai rikon mukamin Daraktan Yada Labarai da Hulda da Jama'a na Kungiyar Gwamnonin, Halima Ahmad, ta fitar tace matukar aka amince da mafi karancin albashin, galibin jihohi zasu yi amfani da yawan kason kudadensu na wata-wata dake zuwa daga asusun tarayya wajen biyan albashin ma'aikata.
Gwamnonin sun roki mambobin kwamitin da su amince da mafi karancin albashin da zai zama mai adalci da dorewa.
Idan ba'a manta ba hadaddiyar kungiyar kwadagon Najeriya ta ki amincewa da tayin naira dubu 60 tare da tsunduma yajin aiki a Litinin din data gabata.
Saidai sun jingine yajin aikin a ranar Talata bayan da gwamnatin tarayya tayi alkawarin biyan mafi karancin albashin daya zarta dubu 60 bayan da suka koma kan teburin tattaunawa.
Dandalin Mu Tattauna