Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

MAFI KARANCIN ALBASHI: Babu Wani Abun Fargaba – Wale Edun


Ministan Kudi da Kula da Tattalin Arziki, Wale Edun
Ministan Kudi da Kula da Tattalin Arziki, Wale Edun

Ministan Kudi da Kula da Tattalin Arziki, Wale Edun, ya ce "babu wani abun fargaba" game da tattaunawar da ake yi tsakanin kungiyoyin kwadago da kwamitin uku kan sabon mafi karancin albashin ma'aikata a kasar. 

Ministan ya bayyana haka ne bayan ya gana da Shugaban Kasa Bola Tinubu a fadar Aso Rock da ke Abuja ranar Alhamis.

Edun da takwaransa na Kasafin Kudi da Tsare-tsaren Tattalin Arziki, Atiku Bagudu, sun gana da Tinubu bayan da shugaban kasar ya karbi bakoncin tawagar hukumar hada-hadar kudi ta kasa da kasa (IFC), memba na bankin duniya, karkashin jagorancin Manajan Darakta, Makhtar Diop, a fadar Aso Villa.

A ranar Talata data gabata ne Ministan yada labarai na Najeriya, Mohammed Idris ya bayyana cewa Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya umurci Ministan Kudi na kasar, Wale Edun, da ya gabatar da tsarin da gwamnati za ta bi yayin da ya ba ministan wa’adin kwanaki biyu domin a gabatar da alkaluman da za a gabatar wa kungiyar kwadagon kan sabon mafi karancin albashi na kasa.

Shugaban ya kuma ce ya kuduri aniyar biyan sama da N60,000 yayin da TUC da NLC suka ce ba su dage kan sai lallai N494,000 ba.

Da aka nemi karin bayani kan sabon mafi karancin albashi, Edun ya gaya wa manema labarai: "Babu wani dalili na tayar da hankali".

Kungiyar Kwadago ta dakatar da yajin aikin sai baba-ta-gani a ranar Talatar da ta gabata, bayan da ta cimma matsaya da gwamnatin tarayya cewa a ci gaba da tattaunawa a kullum har tsawon mako guda har sai an cimma matsaya kan sabon mafi karancin albashin ma’aikata.

Dandalin Mu Tattauna

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG