Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Majalisar Dokokin Najeriya Ta Amince Da Karin Albashi Ga Manyan Alkalai Da Ma'aikatan Shari’a


Majalisar Dokoki ((Facebook/Femi Adesina))
Majalisar Dokoki ((Facebook/Femi Adesina))

Majalisar tarayya Najeriya ta amince da karin albashi da kuma alawus-alawus a dai dai lokacin da sauran ma'aikatan kasar su ke tattaunawa da gwamnati domin neman karin albashi da alawus.

ABUJA, NIGERIA - An dai zartar da kudurin dokar ne bayan amincewa da rahoton kwamitin shari'a da kare hakkin ‘dan Adam da kuma harkokin shari'a, wanda shugaban kwamitin Mohammed Tahir Monguno ya gabatar a gaban Majalisar. Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ne ya gabatar da kudurin ga Majalisar, yan majalisar kuma suka aiwatar da dokar.

Sanata Garba Musa Maidoki
Sanata Garba Musa Maidoki

A hirar shi da Muryar Amurka, Sanata Garba Musa Maidoki daga jIhar Kebbi ta Kudu ya bayyana cewa, gyara albashin alkalan da na ma'aikatan shari'a zai sa alkalai su kare mutuncin shari'a kuma za su kawar da idanun su daga cin hanci da rashawa. Ya kuma kara da cewa majalisa za ta sa ido domin ta tabbatar da cewa an yi adalci wajen ba wa dukan ma'aikata albashin su.

To sai dai ‘dan majalisa mai wakiltan Nasarawa ta tsakiya Ahmed Aliyu Wadada ya bayyana ra'ayi mai babanci kan wannan kudirin dokar inda ya ce a yanayin da ake ciki albashin su yayi daidai, kasancewa, gwamnati ke daukar nauyin dawainyar gidajen su idan suka kai wani matsayi. sai dai ya ce daidai ne a kara albashin saboda dauke hankalin su daga cin hanci da rashawa.

Sanata Ahmed Aliyu Wadada
Sanata Ahmed Aliyu Wadada

Amma ga wata Barista mai zaman kanta Maimuna Yaya Abubakar tana ganin wannan mataki da aka dauka na karin albashi alheri ne kuma abin farin ciki ne, sai dai ta yi kira ga gwamnati ta dubi ma'aikatan ta da irin wannan idanu domin ta kara masu albashi, saboda mutane suna cikin mawuyacin halin a kasar.

A yanzu dai Alkalin Alkalan Najeriya wato CJN zai karbi Naira miliyan 5 da dubu dari uku da tamanin da biyar da ‘yan kai ( 5,385,047.26K) a wata, Alkalan Kotun Koli za su samu jimlar Naira miliyan 4 da dubu dari biyu da goma sha uku da ‘yan kai (4,213,192.54K), sannan shugaban kotun daukaka kara zai rika karban Naira miliyan 4 da dubu dari hudu da saba'in da takwas da ‘yan kai (4,478,415. 78K), Alkalan Kotun Daukaka Kara za su rika karban Naira miliyan 3 da dubu dari bakwai da ashirin da shida da ‘yan kai ( 3, 726,665.40K) a duk wata.

Saurari cikakken rahoton Medina Dauda:

Majalisar Dokokin Najeriya Ta Amince Da Karin Albashi Ga Manyan Alkalai Da Ma'aikatan Shari’a.mp3
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:49 0:00

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG