Majalisar Wakilai Ta Jingine Kudirin Dakatar Da Harajin Tsaron Intanet  

Majalisar wakilan Najeriya (Twitter/ House of Representatives, Nigeria)

Majalisar Wakilan Najeriya ta jingine kudirin dake neman dakatar da batun harajin tsaron intanet daya janyo suka da allawadai daga ‘yan Najeriya

Dan Majalisa Manu Soro, daya gabatar da kudirin gaban majalisar a yau Laraba, yace harajin bai zo a lokaci daya dace ba, duba da mawuyacin halin da ‘yan Najeriya ke ciki.

Ku Duba Wannan Ma CBN Ya Umarci Bankuna Su Caji Kashi 0.5 Cikin 100 A Matsayin Harajin Tsaron Intanet
Ku Duba Wannan Ma Tsarin Harajin Tsaron Intanet Ta CBN Ya Sanya ‘Yan Najeriya Cikin Rudani

Dan majalisar ya kafa hujja da cewar Ofishin Mashawarcin Shugaban Kasa Akan Harkokin Tsaro mukami ne na siyasa: kuma ba shi da ikon tasrifi da kudaden da aka tara.

Saidai, Kakakin Majalisar, Tajuddeen Abbas, ya bukaci ‘yan majalisar su jingine kudirin domin baiwa shugabanninta damar tattaunawa akan hanyar data fi dacewa a shawo kan lamarin.

Kakakin Majalisar Wakilan Najeriya, Tajudeen Abbas

Batun bijiro ta harajin tsaron intanet din ya gamu da suka da cece-kuce tsakanin ‘yan Najeriya da kungiyoyin fafutukar farar hula.

A cewar sanarwar daya rarrabawa bankunan kasar a ranar 6 ga watan mayun da muke ciki, Babban Bankin Najeriyar ya bayyana cewar harajin zai fara aiki ne nan da makonni 2 masu zuwa.