Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Majalisar Wakilai Ta Musanta Zargin Tayin Cin Hancin Binance, Zata Binciki Arcewar Anjarwalla Daga Hannun Jami’an Tsaro


Zauren Majalisar Wakilan Najeriya (Facebook/House of Reps, Nigeria)
Zauren Majalisar Wakilan Najeriya (Facebook/House of Reps, Nigeria)

Hakan na zuwa ne a daidai lokacin da Majalisar ta yanke shawarar gudanar da bincike akan yadda wani babban jami’in kamfanin Binance, Nadeem Anjarwalla, ya arce daga hannun jami’an tsaron Ofishin Mashawarcin Shugaban Kasa Akan Harkokin Tsaro a watan Maris din daya gabata.

Majalisar Wakilan Najeriya ta musanta batun neman cin hanci daga rukunin kamfanonin Binance, sakamakon zargin baya-bayan nan da kamfanin hada-hadar kudin kirfto din yayi.

A jiya Talata ne binace ya bayyana cewar wasu mutane daga Najeriya da ba’a san ko su wanene ba, sun bukaci ya biyasu makudan kudaden intanet “domin taimakawa wajen warware matsalolin kamfanin a kasar”.

Kamfanin ya kara da cewar an tunkari wakilansa bayan da suka bar wurin ganawar da suka yi da kwamitin Majalisar Wakilai akan laifuffukan da suka shafi kudi.

Saidai, a yau laraba Majalisar Wakilan ta musanta zargin bukatar cin hanci daga kamfanin na Binance.

Dan Majalisa, Kama Nkemkanma, ne ya gabatar da kudiri akan batun.

Bayan kafa hujja da batun keta alfarma, dan majalisar ya bukaci majalisar ta sake gayyatar kamfanin domin tantance zargin neman cin hancin.

Kamfanin Binance dai na fuskantar dimbin tuhume-tuhumen aikata manyan laifuffuka a Najeriya bayan daukar tsauraran matakan da gwamnatin tarayyar kasar tayi akan dandalin hada-hadar kudin kirifto a wani yunkuri na kara karfafa takardar kudin Naira.

Tuhume-tuhumen da gwamnatin Najeriya mai ci ke yiwa Binance sun hadar da kaucewa biyan haraji da haddasa rudani a kasuwar musayar kudade da kuma halasta kudaden haram da yawansu ya kai dala milyan 35 da dubu 400.

A watan Maris din daya gabata ne wani babban jami’in kamfanin Binance, Anjarwalla, ya arce daga hannun jami’an tsaron Ofishin Mashawarcin Shugaban Kasa Akan Harkokin Tsaro, Nuhu Ribadu, kamar yadda sanarwar da mai magana da yawunsa, Zakari Mijinyawa, ya fitar ta bayyana.

Anjarwalla na daya daga cikin wadanda gwamnatin tarayya ke zargi a bincikken da take gudanarwa game da ayyukan Binance a Najeriya.

Dandalin Mu Tattauna

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG