An Gudanar Da Zanga-Zangar Tsadar Rayuwa A Ibadan

  • Hasan Tambuwal

Masu zanga-zangar tsadar rayuwa a Ibadan, babban birnin jihar Oyo.

Da sanyi safiyar yau litinin ne darurruwan mutane maza da mata suka yi zanga zanga dauke da kwalaye masu rubutu iri iri suna kokawa game da tsadar rayuwa a kasar.

Hakan na zuwa ne bayan gudanar da irin wannan zanga-zanga a jihohin Kano da Neja, inda mutane da dama suka fito domin kokawa kan matsalar tashin farashin kayan masarufi.

Zanga-zangar tsadar rayuwa a Ibadan, babban birnin jihar Oyo.

A cewar masu zanga-zangar, hauhawar farashin kayan masarufi da rashin daukar kwakkwaran mataki daga bangaren gwamnati ya sanyasu datse manyan hanyoyi da nufin janyo hankalin gwamnatin ta sauraresu.

Wata mata ta roki gwamnati da ta taimaka wa jama'a saboda suna cikin wahala. Tace "abinci ya yi tsada, babu wutar lantarki, babu ruwan fanfo", ta kuma "roki gwamnati ta ceci jama’a".

Ku Duba Wannan Ma Zanga-Zanga Akan Tsadar Rayuwa Ta Sabbaba Rufe Tituna A Birnin Minna

Wani, a cikin masu zanga zangar, yace dalilin da ya sa ya shiga zanga zanga, shine saboda gwamnati ta gaza ba ta yi musu komai ba, kuma abin takaici ne irin halin da suke ciki.

Yadda a ka yi zanga-zangar tsadar rayuwa a Ibadan, babban birnin jihar Oyo.

Yace yawancin masu zanga zanga matasa ne marasa aiki, marasa abinci kuma farashi yayi tashin gauron zabo, wadda hakan ya yi sanadin lalacewar abubuwa.

A saurari cikakken rahoton Hassan Umaru Tambuwal:

Your browser doesn’t support HTML5

An Gudanar Da Zanga-Zangar Tsadar Rayuwa A Ibadan