Hukumomin Amurka Sun Saki Hotunan Hatsarin Da Yayi Sanadiyar Mutuwar Wigwe Da Wasu Mutane Biyar

Wigwe helicopter crash site

Hukumomi a kasar Amurka sun fitar da hotunan wurin da mummunan hatsarin jirgin saman daya kashe Shugaban Rukunin Kamfanonin “Access Holdings” da wasu mutane biyar ya afku.

A cikin hotunan da aka fitar, jami’an hukumar kiyaye afkuwar hatsari ta amurka (NTSB) guda biyu (2) suna duba tarkacen jirgin saman shelkoftan da yayi hatsarin.

Wigwe helicopter crash

A juma’ar da ta gabata, 9 ga watan Fabrairun da muke ciki ne fasinjoji hudu da matuka jirgin saman mai saukar ungulu su biyu suka mutu.

Wigwe plane crash

Hotunan, wadanda aka fitar bayan da Micheal Graham, mamba a hukumar ta NTBS, yace sun ziyarci wurin da jirgin ya fadi tare da zayyana irin ayyukan da suka gudanar cikin kwana guda a inda al’amarin ya faru, suka nuna yadda jami’ai suke nazari akan tarkacen jirgin dake warwatse a wurin.