Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Rasuwar Wigwe: Kamfanin Hannayen Jarin “Access Holding” Ya Nada Agbede A Matsayin Shugaban Riko


Bolaji Agbede
Bolaji Agbede

Kamfanin kula da hannayen jarin rukunin kamfanonin “Access Holding” ya nada Bolaji Agbede a matsayin Shugaban Riko biyo bayan mutuwar Herbert Wigwe.

Wigwe, wanda ya kasance Shugaban rukunin kamfanonin “Access Holdings”, ya mutu ne a wani hatsarin jirgin sama mai saukar ungulu a kasar Amurka a karshen makon daya gabata tare da matarsa da dansa da kuma tsohon Shugaban Hukumar Kula da Musaya ta Najeriya, Abimbola Ogunbanjo.

Kimanin kwanaki biyu bayan afkuwar hatsarin jirgin saman daya gigita bangaren banki da mutane da dama a Najeriya, Access Holding ya sanar da sunan Agbede a matsayin sabon Shugabansa.

Sanarwar da sakataren rukunin kamfanonin Access Holdings Sunday Ekwochi ya fitar tace, biyo bayan sanarwa da muka fitar a ranar 11 ga watan febrairun shekarar 2024, a yau kwamitin daraktocin access holdings ya sanarda nadin uwargida bolaji agbede a matsayin shugabar riko sakamakon mutuwar da tsohon shugaban kamfanin yayi a ranar tara (9) ga watan febrairun shekarar 2024.

“Nadin ba zai tabbata ba har sai an samu amincewar babban bankin najeriya.”

Kafin nadin, Agbede ta kasance babbar daraktar da aka kafa kamfanin da ita mafi girman mukami dake kula da sashen tallafawa harkokin kasuwanci.

Dandalin Mu Tattauna

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG