Musulman Najeriya Sun Kashe Dala Biliyan 107 Wajen Sayen Kayayyakin Halal A Shekarar 2022

NIGER: Kungiyar matasa musulmi ta yi bude baki da kiristoci

Rahoton kasuwar Kayayyakin halal na 2023 ya nuna cewa Musulmai a fadin duniya sun kashe kudi da ya kai dala tiriliyan biyu da digo uku ($2.3trillion) wajen sayen abubuwan halal da suka hada da abinci, sutura, yawon shakatawa, magunguna, kayan kawa, da kuma tafiye-tafiye a shekarar 2022.

Musulmai a fadin duniya a kowanne lokaci na kaffa-kaffa wajen siyen abinci, sutura, magunguna don ganin basu yi amfani da wani abu da ya sabawa addinsu ba. Wannan ne ya assasa batun kayayyakin halal a kasashen duniya.

Najeriya na cikin kasashen dake amfani da kayayyakin halal, hakan ne yasa aka sami kasuwar halal. Rahotan da aka gabatar na kasuwar ta halal ta shekarar 2023 a Abuja babban birnin Najeriya na nuni da cewa, Musulmi a Najeriya sun kashe Dala biliyan 107 a shekara ta 2022.

“Musulman Najeriya sun kashe kudin daya kai Dala Biliyan dari da bakwai ($107bn) wajen Siyen Kayayyakin halal wanda hakan ke nuna cewa Najeriya nada Kashi hudu da digo bakwai (4.7%) na yawan kudaden da aka kashe a Siyen kayan halal a duniya, to amma Idan aka kwatanta da wasu kasashen nahiyar Afrika Najeriya nada Kashi ashirin da biyu da Kashi bakwai (22.7%) na yawan kudin da musulman nahiyar ke kashewa wajen siyen kayan halal.

Taron Nunin Kaya Na Mata Musulmi A Abuja, Najeriya, Lahadai 27 Afrilu 2014

Kasar Masar dai ita ce a mataki na farko a nahiyar Afrika a bangaren kasuwar kayayyakin halal a Afrika da Najeriya ke biye a mataki na biyu. A cewar shugaban Dinar-Standard Rafi-Uddin Shikoh yayin gabatar da rahoton.

Najeriya dai ita ce kasa ta takwas cikin kasashen da suka fi kashe kudi wajen sayen kayayyakin halal a fadin duniya.

Rahoton na nuni da cewa, Kasar Indonesia ce a mataki na farko inda yan kasar suka kashe dala biliyan dari biyu da goma sha shida ($216billion) wajen sayen kayayyakin halal.

Kasar Iran ce ta biyu inda Musulman kasar suka kashe dala biliyan dari da sittin da takwas ($168billion).

Kasar Masar wato Egypt da take mataki na uku da Musulman kasar suka kashe dala biliyan dari da sittin da bakwai ($167bn).

Kasar Bangladesh na mataki na hudu saboda Musulman kasar sun kashe dala biliyan dari da sittin da biya ($165bn)

Saudiyya ita ce kasa ta biyar, inda Musulman kasar su ka kashe dala biliyan dari da arba’in da shida ($146bn).

Kasar Turkiyya dake mayaki na shida. Musulman kasar suma sun kashe dala biliyan dari da arba’in da shida ($146bn).

Kasa ta bakwai ita ce kasar Pakistan a yayin da Musulman kasar suka kashe dala biliyan dari da talatin da tara ($139bn) wajen sayen kayan halal.

Najeriya ce kasa ta takwas domin kuwa musulama kasar sun kashe dala biliyan dari da takwas ($108bn) wajen sayen kayan halal.

Kasar India ce ta tara a yayin da Amurka ke mataki na goma.”

Rahoton dai ya nuna yadda Najeriya ke asarar kudin shiga musamman yadda shigowa da kayan halal kasar ya ninka yawan wanda kasar ke fitarwa zuwa kasashen musulmai a fadin duniya.

Rahoton ya bayyana cewa, “Najeriya ta shigo da Kayayyakin halal da kudinsu ya kai dala biliyan shida da digo ashirin da shida ($6.26bn). Amma kasar na fitar da kayan halal da ya kai dala miliyan dari uku da Saba’in da tara ($379million) wanda shine kashi 0.1% na yawan kudin kayayyakin halal da ake fitarwa kasashen duniya.”

Musulmi daga kasashe dabam-dabam na duniya su na yin buda baki a rana ta biyu da fara azumi a Masallacin Dirah dake Riyadh, babban birnin Sa'udiyya, Alhams 12 Agusta, 2010.



Kayayyaki halal da Musulman Najeriya suka fi saya a shekarar 2022

Abinci
Musulman Najeriya sun kashe dala biliyan casa’in da uku ($93bn) wajen sayen abincin halal, wanda shine kashi bakwai (7%) na yawan kudin da Musulman duniya suka kashe wajen sayen abincin halal a shekarar 2022. Sannan ana sa ran ya kai dala dari da arba’in da takwas ($148bn) nan da shekarar 2027.

Sutura
Musulman Najeriya sun kashe kudin da ya kai dala biliyan shida da digo biyu ($6.2bn) wajen sayen kayan sawa na halal.

Tafiya-Tafiye
Musulman Najeriya sun kashe dala biliyan uku da digo shida ($3.6bn) wajen tafiye-tafiye ta hanyar amfani da kamfanoni na halal.

Kayan kwalliya
Musulman Najeriya sun kashe dala biliyan daya da digo takwas ($1.8bn) wajen sayen kayan kwalliya na halal, ana kuma yakinin zai karu zuwa dala biliyan biyu da digo takwas ($2.8bn) nan da shekarar 2027.

Magunguna
Musulman kasar suka kashe dala miliyan dari bakwai da hamsin da bakwai ($757million) wajen sayen magunguna na halal.