Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yar Tallar Tufafin Kawa Naomi Campbell Tana Shirin Bayar Da Shaida A Shari'ar Charles Taylor


Naomi Campbell zata bayar da shaida game da dutsen Daiman da ake zargin Taylor ya taba ba ta, a bayan da alkalai suka yi watsi da yunkurinsa na karshe na hana ta bayar da shaida.

Alkalai na Kotu ta Musamman mai bin kadin Laifuffukan Yaki a kasar Saliyo sun yi fatali da yunkurin karshe da tsohon shugaban Liberiya, Charles Taylor, yayi na hana 'yar tallar kayan tufafi na kawa, Naomi Campbell, bayar da shaida alhamis din nan a shari'ar da ake yi masa ta aikata laifuffukan yaki.

Ana tuhumar Taylor da samar da makamai ga 'yan tawaye a lokacin yakin basasa na kasar Saliyo, su kuma su na ba shi duwatsun da aka lakaba wa suna "Daiman na Jini", watau sunan da ake ba duwatsun daiman da ake tonowa ana saidawa domin rura wutar yaki.

Charles Taylor a cikin kotu
Charles Taylor a cikin kotu

Masu gabatar da kara su na son yi ma Naomi Campbell tambayoyi game da zargin cewa Charles Taylor ya ba ta kyautar irin wannan dutse a lokacin wata liyafar cin abincin daren da Nelson Mandela ya shirya a Afirka ta Kudu a shekarar 2007.

Ita da Taylor duk sun musanta wannan zargi. Lauyoyinsa sun yi korafin cewa masu gabatar da kara ba su mika musu bayanin irin abubuwan da ake tsammanin zata bayar da shaida a kai ba.

Wata tsohuwar manaja ta Campbell, Carole White, da kuma jaruma Mia Farrow, sun ce su na sane da wannan kyauta da Taylor yayi ma Campbell. Su biyun sun yarda a kan za su bayar da shaida domin radin kansu a gaban wannan kotu dake birnin Hague a kasar Netherlands.

XS
SM
MD
LG