Tuni dai shirye-shiryen sayar da gidajen ma'aikatan kwalejin kimiya da fasaha da ke Kaduna wato KADPOLY ya yi nisa, duk kuwa da turjiyar da kungiyar malaman Kwalejin ke yi cewa ba ta amince ba.
Engr. Abubakar Jibril Abdullahi, shine shugaban kungiyar malaman kuma ya ce su na da dalilan kin amincewar da su ka yi.
Ya ce gidajen ma'aikatan kwalejin kimiya da fasaha na Kaduna ba mallakin gwamnatin tarayya ba ne, saboda haka bata da hurumin sayar da gidajen.
Duk da wannan rashin amincewa ta malaman Kwalejin KADPOLY, ita kungiyar manyan ma'aikata da kuma ta kananan ma'aikatan kwalejin kimiya da fasaha na KADPOLY, sun ce su na goyon bayan sayar da gidajen, inji shugaban kungiyar manyan ma'aikata, Malam Ibrahim Abdussalam Abubakar.
Malam Abubakar ya ce tun da dai ma'aikatan kwalejin za a sayarwa to suna goyon baya kuma za su tabbatar da ba a sami matsala ba.
Sai dai shugaban kungiyar malaman Kwalejin ta KADPOLY ya ce akwai matsalar tsaro ma game da sayar da wadannan gidaje.
Saurari rahoton a sauti:
Your browser doesn’t support HTML5