Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Najeriya Na Da Karancin Kere-Keren Fasahohin Zamani- Farfesa Bugaje


Wani malami, Lawal Olaide da dalibarsa Adebola Duro-Aina da ta hada janareto mai samar da wutar lantarki ta hanyar amfani da fitsari a Legas (Hoto: AP)
Wani malami, Lawal Olaide da dalibarsa Adebola Duro-Aina da ta hada janareto mai samar da wutar lantarki ta hanyar amfani da fitsari a Legas (Hoto: AP)

“Wanda ya fito da kwarewa ta sana’ar hannu, ya fi mai digri daukan albashi. Shi ya sa mu ke kira ga matasa da iyaye su gane cewa, mu dawo daga rakiyar wai sai kowa ya yi digiri."

A Najeriya, masana a fannin kimiyya na ci gaba da kira ga jami’o’i da kwaleji-kwalejin kasar, da su mayar da hankali wajen horar da dalibai a fannin kere-kere da sana’o’in hannu.

Yayin wata hira ta musamman da Muryar Amurka, Shugaban hukumar kula da ilimin kimiyya da fasaha a Najeriya ta NBTE, Farfesa Idris Bugaje, ya ce lokaci ya yi da Najeriya za ta fara kere-keren da za ta iya nuna kwarewarta a duniya.

“Wanda ya fito da kwarewa ta sana’ar hannu, ya fi mai digri daukan albashi. Shi ya sa mu ke kira ga matasa da iyaye su gane cewa, mu dawo daga rakiyar wai sai kowa ya yi digri, ka je ka koyi sana’a, kai ko digri ka yi ka je ka koyi sana’ar hannu.” In ji Farfesa Bugaje.

Ya kara da cewa, “Matatar mai da Dangote ya gina a Lekki na jihar Legas, wacce duk duniya babu kamarta, amma wajen ma’aikata kusan dubu biyu ya dakko daga India, su suke ke yin walda, su suke harhada pipe suke ayyuka na sana’ar hannu, wanda ya kamata a ce matasan Najeriya aka dauka.”

A cewar Farfesa Bugaje, abin takaici shi ne, gwamnatin ta ba jami’o’i biliyoyin kudade amma har yau babu wata fasaha da za a yi tunkaho da ita.

“Idan ka je Korea, suna da LG, suna da Samsung, idan ka je Japan suna da Honda, suna da Toyota, in ka je Jamus ga Mercedes Benz, in ka je Ingila ga Leyland. Duk wata kasar duniya suna da wata fasahar da suke tunkaho da shi.”

“Mu kuma nan Najeriya muna ba jami’o’ biliyoyi duk shekara, amma yau babu wata jami’a da ta fitar da wata fasaha da za a ce wannan ta Najeriya.”

Hakan ya sa hukumar ta NBTE a cewar Bugaje, ta kira kwalejojin na fasaha da su zo su baje irin bajintarsu, kuma an samu na’aurori sama da goma da aka hada yana mai kira ga ‘yan kasuwa da su je su ganewa idonsu don amfaninsu.

Sai dai a lokuta da dama, ‘yan kasuwa da masu amfani da kayayyakin kasashen waje, kan yi korafin cewa kayan kasar ba su da ingancin na kasashen ketare, dalili da ya sa Kenan suka fi raja’a a kansu.

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG