NEMA Na Wayar Da Kan Al'umma Kan Ambaliyar Ruwa Da Ka Iya Faruwa

Ambaliyar Ruwa

Hukumar bada agajin gaggawa ta kasa, NEMA, ta dukufa wajen wayar da kan al’umma matakan da zasu bi wajen kare kansu daga bala’in ambaliyar da ruwan sama ka iya haddasawa a jihohi.

Fadakarwar ta biyo bayan sakin ruwa daga madatsar ruwa ta Lagdo, dake kasar Kamaru, lamarin das au da dama ke janyo rasa rayuka da asarar dukiya a wassu jihohin Najeriya.

A cewar jami’in dake kula da jihohin Binuwai, Nasarawa da Filato a hukumar baga agajin gaggawa ta kasa, Mr Lugard Bijimi Slaku, barnar ta fara aukuwa a jahar Adamawa don haka jama’a su dau matakan kare kansu.

Sarakunan gargajiya da masu unguwanni nada gagarumin gudunmowa wajen fadakadda al’umma illar da toshe magudanan ruwa keda shi.

Madam Henrietta Ibrahim, shugaban gidan rediyon tarayya na Highland FM dake nan Jos, ta ce kafofin yada labarai na kokari kwarai wajen fadakadda jama’a batun ambaliya.

Darakta a ma’aikatar yada labaran jahar Filato, Harris Dawurang yace suna shiga lungu da sako suna bayyana wa mutane yadda zasu kare kansu daga ambaliyar ruwa.